17 Agusta 2026 - 20:25
Source: ABNA24
Na’urorin Buga Takardu 61 Suka Samu Lahani Ko Lalacewa Gaba Day A Yakin A Iran

Rahotannin al'adu sun bayyana cewa madaba’ar takardun da yawa a sassa daban-daban na Iran sun fuskanci lalacewa daban-daban sakamakon yaƙin da aka kakabawa Iran na uku.

Kamfanin Dillancin Labarai na Ahlul-Bayt (a.s) – ABNA – ya bayar da rahoton cewa: Babban daraktan harkokin bugu da yada littafai na ma'aikatar al'adu da shiryarwar Musulunci, bayan sanar da tsagaita wuta, ya shirya jerin asarar da wanna sana’a ta gamu da ita, kuma an mika shi ga sashen hulɗa da jama'a na ma'aikatar don aikawa ga ofishin mataimakin farko na shugaban ƙasa.

Daga cikin madaba’ai 61 da aka kai hari a lokacin "Yakin Ramadan," madaba’a 3 sun lalace gaba ɗaya, yayin da barnar a sauran wuraren ta bambanta tsakanin ƙarama da babba, wanda jimillar asarar ta kai biliyan 660 Tuman.

Tare da bin diddigin da kamfanin dillancin labarai na "Tasnim" ya yi, da kuma kafa "Kwamitin Sauƙaƙe asarori" a ma'aikatar masana'antu, ma'adinai, da kasuwanci don tallafa wa wuraren da suka lalace, an warware matsalolin waɗannan nau’rori. Shirye-shiryen tallafin da aka tsara sun haɗa da: raba haraji a kashi-kashi, dage biyan kuɗaɗen inshora na watanni 6, ba da sauƙaƙewar lamuni mai rahusa a hanya mai sauri, keɓe filaye a farashi mai ƙarfafawa a kan hanyar (Qom - Tehran), tare da wasu hanyoyin tallafi da aka keɓe ga madaba’oin da yaƙin ya shafa.

………………

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha